Shugaba Buhari a ranar Laraba 14 ga watan Disamba ya gana da shugaban kasar Amurka Joe Biden a birnin Washington DC.
Hotunan da fadar shugaban kasa ta raba sun nuna shugaban kasar a ganawarsa da Biden da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a fadar White House a gefen taron shugabannin Amurka da Afirka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: Jakadan Najeriya A Kasar Spain Ya Rasu
Taron na Amurka da Afirka, wanda aka fara a shekarar 2014, shi ne taro mafi girma na kasa da kasa da aka gudanar a Washington tun bayan barkewar annobar COVID-19.
Sannan kuma alƙawarin da gwamnatin Amurka ta yi na haɓaka tasirinta a Afirka kusan shekaru goma.
Taron, a cewar gwamnatin Amurka, “zai nuna dawwamammen sadaukarwar Amurka ga Afirka, kuma zai nuna mahimmancin dangantakar Amurka da Afirka, da kuma kara yin hadin gwiwa kan muhimman abubuwan da suka sa a gaba.”
A wani labarin kuma, Hukumar NDDC Ta Raba Kayayyakin Agaji Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
Hukumar raya yankin Neja Delta ta fara rabon kayan agaji ga al’ummar da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Imo. Kamar yadda Punch ta ruwaito.
Da yake jawabi yayin mika ragamar gudanarwa a ofishin NDDC na jihar Imo, dake Owerri, a ranar Larabar, mukaddashin Manajan Daraktan hukumar, Emmanuel Audu-Ohwavborua, ya ce hakan na daga cikin matakan da hukumar ta NDDC ta dauka na rage radadin al’ummar yankunan da abin ya shafa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hukumar NDDC, Dokta Ibitoye Abosede, ya fitar kuma ya rabawa wa manema labarai a Fatakwal ranar Laraba.
Audu-Ohwavborua, wanda ya samu wakilcin Daraktan Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jama’a, Dokta George Uzonwanne, ya ce matakin na ci gaba da shiga tsakani domin tallafawa al’umma.