Izuwa yanzu Aƙalla Mutum Sittin ne giwaye suka kashe a dai dai lokacin da ake da samun rashin jituwa tsakanin giwaye da mutane a kasar Zimbabwe, kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin ƙasar ya bayyana.
Kasar Zimbabwe ita ce kasa ta biyu a wurin yawan giwaye a duniya bayan ƙasar Botswana, inda ƙasar take da yawan giwaye kimanin dubu ɗari a ƙasar.
Kuma ita keda kusan kashi ɗaya bisa Uku na yawan giwayen da ke nahiyar Afirka.
Zimbabwe Bakamar sauran wasu ƙasashen duniya ba ne, inda ake samun masu farautar dabbobi ba bisa ka’ida ba, inda yawan giwayen kasar ta Zimbabwe ke da da ƙaruwa da kashi biyar cikin dari a duk shekara.
Kamar yadda Mangwana ya wallafa a shafin Twitter ya ce zirga-zirga da Giwaye ke yi tayi sanadiyar lalata wasu wurare wanda yanzu haka suke ƙoƙarin kutsawa izuwa wuraren da mutane ke zaune tare da kokarin farmusu wanda hakan ke sanya mutane yunkurin kare kansu har hakan kan haifar da jima wasu giwayen.
Mangwana ya ce fadace fadace tsakanin dabbobin da mutane a yankin ya munana , inda a wannan shekarar a ƙalla mutum 60 suka rasa rayukansu, yayin da 50 Kuma suka samu rauni.
Yayinda A shekarar 2021 an tabbatar da cewa giwayen sun kashe mutum 72 a ƙasar ta Zimbabwe.
Masana dai na ganin cewa karuwar yawan al’umma da talauci na daga cikin dalilan da ke sanya mazauna yankunan karkara suyi hijira zuwa wuraren da ke sanyasu suyi fada da giwayen.
Kasar Zimbabwe na da yawan jama’ar da yakai miliyan goma sha biyar 15, wanda ke ƙaruwa da kashi 1.5 a duk shekara.
Wani masani harakar dabbobin dake aiki a gidan ma’aikatar kula da dabbobi ta kasar Tinashe Farawo ya fadawa kamfanin dillanci labaria na AFP cewa sai an rage yawan giwayen in ana son fadan ya ragu.
Yace akwai yiyuwar fadan ya karu a lokacin rani lokacin da dabbobin zasu rinka fita neman abinci da ruwan sha.
Ya Kuma yi kargadi cewa, Tuni dai aka haramta fitar da giwaye awajen kasar ta Zimbabwe.
To amma yanzu gwamnatin kasar na duba yiyuwar bayar da lasisin farauta domin ci-gaba da kula da giwayen.