Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ba zai yi nadamar nada shi a matsayin minista a majalisarsa ba.
Majiyar JARIDAR DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Wike ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da tambayoyi a zauren majalisar dattawa yayin tantance ministocin a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN: Zanga-Zanga: NLC, TUC Sun Shiga Ganawa da Wakilan FG A Fadar Gwamnati
Wike ya ce, ”Na gode wa shugaban kasa da ya zabe ni. Na yi imani da sanin irin yunwar da shugaban kasa ke fama da shi wajen magance matsalolin Najeriya, ba mu da wani zabi illa mu ba shi goyon bayan da ake bukata.
“Sannan kuma ina mai tabbatar muku da cewa idan aka tabbatar da ni, ba zai taba yin nadamar zabe na ba a kowane irin matsayi.”
Wike bayan ya fitar da bayanan karatunsa da kuma nasarorin da ya samu, ya lura cewa kishinsa ga Najeriya ne ya sa ya amince da tayin minista.
Wike, wanda aka tantance a yau shi ne kadai jigo a jam’iyyar PDP da aka zaba a cikin jerin sunayen ministocin da shugaban kasa ya aika wa majalisar dattawa a ranar Alhamis din da ta gabata.
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Umurci Cibiyoyin Tarayya Su Dakatar da Karin Kudade
Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Litinin ya umurci hukumomi a dukkan makarantun gwamnatin tarayya da su guji karin kudaden da ake biya ba bisa ka’ida ba, domin karin da ake yi musu iyaye da dalibai zasu fuskanci wahalhalu da yawa.
Ya kuma amince da samar da motocin bas ga dukkan daliban jami’o’i da kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi a fadin kasar nan.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rattabawa hannu a ranar Litinin mai taken ‘Gwamnatin taryya a shirye ta ke ta samar da motocin bas ga daliban manyan makarantu, ta cire takunkumin da aka sanya wa daliban kan lamuni.