Tinubu na iya bayyana sunayen ministoci ranar Talata – Bashir Ahmad
Bashir Ahmad, mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin sadarwa ta zamani ya yi ikirarin cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bayyana jerin sunayen ministocin da ya so ya yi aiki dasu a ranar Talata.
Ahmad ya bayyana hakan ne a daren ranar Litinin a shafin sa na Twitter.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yadda Gobarar Tankar Mai Ta Hallaka Mai Juna Biyu Da ‘Ya’yanta 3 Da Wasu —Shaidu
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa shugaban kasa ya rage kwanaki 5 kafin cikar kwanaki 60 na gabatar da jerin sunayen ministocinsa domin tantancewa da tabbatar dasu a majalisar wakilan Kasar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar na 1990 da aka yi wa gyara ya tabbatar.
Ahmad ya ce a ranar Talata ne za a bayyana jerin sunayen a majalisar dattawa, muddin ba a samu sauyi ba.
” Majalisar Dattawa za ta sanar da jerin sunayen ministocin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar a gobe Talata”, in ji shi.
Ana sa ran jerin sunayen ministocin zai hada da akalla mutum daya da aka zaba a fadin Jihohi 36.
DAILY POST ta tuna cewa Buhari ya nada ministoci 44 watanni 6 bayan rantsar da shi a shekarar 2015.
A wani labarin kuma:Yadda Barayi Suka Sace Jariri A Shagon Mahaifiyar Sa
Rahotanni sun ce an sace wani jariri dan watanni 6 mai suna Chinedu Chukwueke a shagon mahaifiyarsa da ke Kasuwar Kure Ultra-Modern Market, Minna, Jihar Neja.
Mahaifin yaron mai suna Chikezie Stanley Chuks ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook