Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kammala shirye-shiryen hada tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Sanata Godswill Akpabio, da Sanata Jibrin Barau a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Akpabio da Barau na daga cikin ‘yan takara 9 da za su fafata a zaben shugabancin majalisar dattijawan a majalisa ta 10, wanda ake sa ran za a kaddamar da ita a ranar 13 ga watan Yuni.
KU KARANTA: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Gurfanar Da Sanin Doka Bisa Zargin Aika Laifin Sata
Majiya mai tushe ta shaida wa jaridar cewa zababben shugaban kasar wanda ya dawo kasar a ranar Litinin bayan shafe kwanaki 34 a kasar waje, ya bayyana matakin nasa ga Akpabio da Barau a wani taro da aka gudanar a Abuja.
A ranar Talata ne tsohon gwamnan jihar Legas ya gana da Akpabio, Barau, Sanata Opeyemi Bamidele da kuma gwamnan jihar Ekiti, Biodun Oyebanji.
Majiyoyin sun ce yayin ganawar da suka yi ta kasance a wurin zababben shugaban kasa, an bukaci Barau ya janye kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin majalisar dattawa domin samun hadin kan kasa, daidaito da kuma daidaita addini.
Wani dan majalisa daga Kudu ya ce an yi nasara a kan Barau ya sadaukar da burinsa domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Zababben shugaban kasar ya shaida wa Barau cewa ya cancanta sosai a wannan aiki amma ya yi watsi da burinsa na fitowar Kirista domin baiwa gwamnatinsa damar fara aikin da ya kamata.
A wani labarin kuma: Tinubu A Shirye Yake Domin Yiwa Yan Najeriya Aiki – APC
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya tabbatar wa ‘yan kasa cewa, zababben shugaban kasa na cike da koshin lafiya, kuma a shirye yake wajen mulkin kasar nan cike da kwarewa da kuma qwarin gwiwar samar da ci gaba mai dorewa, gabanin bikin rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.
Sanata Adamu ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar wata kungiya mai rajin tabbatar da Najeriya karkashin kungiyar ‘yan asalin kasar nan a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Abuja jiya Alhamis.