Tinubu Ya Amince Da Kafa Asusun Samar da Ababen More Rayuwa Ga Jihohi
A wani mataki na dakile illolin cire tallafin man fetur, Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa Asusun Tallafawa Jihohi (ISF) ga Jihohi 36 na Tarayya.
An sanar da amincewar ne a taron wata-wata na Kwamitin rarraba albarkatu na kasa (FAAC) a ranar Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Arewa Na Cigaba Da Nuna Bukatar Su Ta Sakin Abdulrasheed Bawa
Asusun samar da ababen more rayuwa zai baiwa Jihohi damar shiga tsakani da saka hannun jari a muhimman fannonin sufuri, noma, kiwo da hanyoyin kiwon lafiya da ilimi.
Haka kuma zai inganta gasa ta fuskar tattalin arziki, samar da ayyukan yi da samar da wadatar tattalin arziki ga ‘yan Najeriya.
Kwamitin zai kuma kuduri aniyar ajiye wani kaso na kudaden da ake rabawa duk wata domin rage tasirin karin kudaden shiga da ake samu ta hanyar cire tallafin da hada kan kudaden musaya a kan samar da kudi, da hauhawar farashin kayayyaki da kuma farashin canji.
Ta ce daga cikin kudaden shiga na watan Yunin 2023 da za a raba na Naira Tiriliyan 1.9, Naira biliyan 907 ne kawai za a raba a tsakanin matakan gwamnati uku, sauran kuma za a yi amfani da su wajen cire kudi na doka.
Wadannan tanadin za su taimaka wa yunƙurin Asusun Tallafawa Kayan Aiki (ISF) da sauran matakan da ake da su da kuma shirye-shiryen kasafin kuɗi, duk da nufin tabbatar da cewa cire tallafin ya juya zuwa ga ci gaban rayuwa da yanayin rayuwar ‘yan Najeriya.
Kwamitin ya yaba wa Tinubu kan matakin da ya dauka na cire tallafin man fetur, da ma mahimmaci, na ba da goyon bayan da ya dace ga Jihohin domin dakile illolin cire tallafin ga ‘yan Nijeriya.
A wani labarin kuma:Oyo Ta Rufe Asibito 5 Masu Zaman Kansu Kan Rashin Kwarewa
Gwamnatin jihar Oyo ta bayyana cewa ta rufe cibiyoyin lafiya akalla biyar masu zaman kansu a Ibadan babban birnin jihar.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ga Majiyar mu a ranar Juma’a.