Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano. Kamar yadda Daily Trust ta ruwiato
Tinubu wanda ya kai ziyarar kwanaki 2 a Kano, ya bayar da gudunmawar ne a lokacin liyafar cin abinci da kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano ta shirya masa domin karrama shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-Dumi: ASUU Ta Daukaka Kara Kan Hukuncin Kotun NIS
Ya ce sun bayar da tallafin ne domin taimakawa da rage radadin ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin da abin ya shafa.
Dimokiradiyya ta ruwaito hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ta bayyana cewa an samu ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 19 cikin 44 na jihar inda mutane 23 suka mutu, 106 suka jikkata, sannan gidaje 12,919 suka lalace yayin da gonaki 14, 496 suka lalace a kananan hukumomin biyar.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi alkawarin sake mayar da masana’antun da ake da su tare da mayar da su a matsayin tushen ci gaban masana’antu da bunkasa ba kawai ga Arewa ko Kano ba har ma da kasa baki daya.
Ya kuma yabawa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa kokarinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar, inda ya bayyana gwamnan a matsayin “aboki kuma amintaccen abokin tarayya”.
Ya kuma yi wa ’yan kasuwar alkawarin cewa zai samar da yanayin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.
Masu jawabai a cikin ‘yan kasuwar sun gabatar da tsarinsu ga Tinubu, inda suka yi kira gare shi da ya mai da hankali kan wutar lantarki saboda an rufe masana’antu da yawa saboda rashin isasshen wutar lantarki.
A WANI LABARIN KUMA: Yan bindiga Sun Sake Garkuwa Da Hamshakin Dan Kasuwan Jihar Cross Rivers
Wata mota ta murkushe wata yarinya ‘yar shekara biyar a hanyar sabon titin filin jirgin sama na Calabar.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar jim kadan bayan da aka yi garkuwa da wani dan kasuwa yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin titin filin jirgin