Tinubu ya san ƴan Najeriya na shan wahala – Tsohon dan takarar shugaban kasa a APC
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Cif Stanley Osifo, ya ce shugaba Bola Tinubu ya fahimci cewa ‘yan Najeriya na cikin wahala.
Osifo ya ce Tinubu na yin duk mai yiwuwa don gyara kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zanga-zanga ta barke a Ibadan kan tsadar rayuwa
Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a ranar Litinin, tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce: “Kowane dan Najeriya yana da abu daya da zai yi magana a kai yanzu kan shan wahala.
“Wannan abu mai kyau shi ne ko shugaban kasa ya amince da matsalolin kuma ya fahimci halin da ‘yan Najeriya ke ciki a yanzu.
“Ya amince da matsalar a ganawarsa da gwamnonin karshe. Ya ba da tabbacin cewa da lokaci, abubuwa za su daidaita.
“Bai kamata ‘yan Najeriya su firgita ba saboda abin da muke ciki a yanzu lokaci ne, kuma na yi imanin wannan matakin zai wuce nan ba da jimawa ba.”
Ya kara da cewa al’amura ba su yi wa ‘yan Najeriya sauki ba sakamakon halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, yana mai jaddada cewa shugaban kasar ba ya barci a kan komai.
Ya kara da cewa: “Shugaban kasa na kokarin ganin ya daidaita tattalin arzikin kasar kuma ya yi wasu kalamai da tsoma baki kan yadda za a ba da tallafi ga jama’a.
“Na yi imanin cewa Shugaban kasa ya san abin da ke faruwa a yanzu kuma yana yin duk mai yiwuwa don ganin yadda za a magance matsalolin.
“Har ila yau, a bar shugaban kasa da gwamnoni da shugabannin kansiloli su ba da fifiko kan al’amuran da ke addabar talakawan Najeriya.
“Dole ne su magance abubuwa kuma su tabbatar da cewa ‘yan Najeriya ba su sake yin kuka ba.
“Ya kamata kowa yasan cewa ‘yan Najeriya na cikin wahala, don haka akwai bukatar a daina kashe kudi.
A wani labarin kuma:Da duminsa: EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, na tuhumar tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, kan wasu makudan kudade da suka kai biliyoyin naira a lokacin da yake kan mulki.
An ga tsohon gwamnan ya isa ofishin EFCC na Ilorin a safiyar ranar Litinin.