Tinubu zai halarci bikin rantsar da Bassirou Faye a matsayin shugaban kasar Senegal
Shugaba Bola Tinubu na shirin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Faye a matsayin babban shugaban kasa a Dakar ranar Talata bisa gayyatar da kasar da ke yammacin Afirka ta yi masa.
Kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya bayyana a ranar Litinin a Abuja cewa shugaban zai bar Abuja zuwa Dakar ranar Talata.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yadda Ƴan Sanda suka kama barawon babur bayan mahaifinsa ya kai kararsa a Kaduna
Mista Tinubu, shugaban kungiyar ECOWAS na shugabannin kasashe da gwamnatoci, zai bi sahun sauran shugabannin yankin a wajen taron.
Ministan harkokin wajen kasar, Ambasada Yusuf Tuggar da wasu manyan jami’an gwamnati ne zasu raka shi a wannan tafiyar.
Ana sa ran shugaban zai dawo Najeriya bayan kammala rantsar da shi, in ji Mista Ngelale.
A wani labarin kuma:Yadda Hatsarin Mota ya hallaka mutane 13 ya jikkata guda 2 a Kogi – FRSC
Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, ta bayyana a ranar Litinin cewa mutane 13 ne suka mutu yayin da biyu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Kogi.
Samuel Oyedeji, Kwamandan Hukumar FRSC ta Kogi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na daren ran Lahadi.