Wata matar aure mai suna Aminat Garba da ke neman a raba auren ta, ta shaida wa wata kotun Area Court da ke Ilorin a ranar Litinin cewa mijinta Dauda Garba ba ya kula da ita da ‘ya’yansu biyar, Vanguard ta rawaito.
Mai shigar da karar ta shaidawa kotun Area Court dake Centre-Ojagboro cewa ta gaji da aurenta da wanda ake kara saboda rashin bata kulawa.
KARANTA WANNAN: Hajjin 2023: NAHCON Ta Sanya Ranar Kammala Jigilar Alhazan Najeriya Zuwa Gida
“Ba ya ciyar da ni da yara, kuma ba ya kula da mu, duk da haka yana jefa rayuwata cikin hatsari,” kamar yadda ta shaida wa kotun.
Sai dai wanda ake kara ya shaidawa kotu cewa baya son ya saki matar tasa yana matukar kaunarta.
“Ba na son na saki matata, Allah ya abarkaci aurenmu da ‘ya’ya shida, daya ya rasu, saura biyar.
“Ba na son yarana su fuskanci rashin uwa a gida,” in ji shi.
Garba ya ce yana azurta iyalin nasa gwargwadon iyawarsa.
“’Yan uwana sun fara yunƙurin yin magana da matata don sulhunta mu kan rashin fahimtar juna a gaban kotu,” in ji shi.
Alkalin kotun, Aminullahi AbdulLateef, ya ce da alama wanda ake kara ba ya sha’awar auren kamar yadda ya yi ikirari, la’akari da yadda yake magana.
“Kotu ba za ta iya umurtar wanda ta shigar da kara ta so wanda ake kara da karfi ba, ya kamata wanda ake kara ya san yadda yake da kuma halinsa wajen sasantawa.
“Amma ko wanda ake kara yana da gaskiya da ikirarin neman sulhu ko a’a, kotu na da sha’awar sasantawa,” in ji AbdulLateef.
Daga nan ne alkalin kotun ya dage cigaba da sauraren karar har zuwa ranar 6 ga watan Satumba, domin samun rahoton sasantawa.
A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Bukatar Gwamna Ta Nada Masu Bada Shawara Na Musamman
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da bukatar Gwamna Abba Kabir-Yusuf na nadin mukamai na musamman guda 20.
Kakakin majalisar, Ismail Falgore ne ya karanta wasikar bukatar gwamnan a zauren majalisa a ranar Litinin a Kano.