Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, a ranar Asabar, ta samu nasarar damke wani magidanci mai suna Aminu Abubakar, mai shekaru 56, bisa zarginsa da lakadawa matarsa mai shekaru 38 da haihuwa dukan tsiya,Punch ta rawaito.
Wanda ake zargin, mazaunin Lelewaji, Shagari Phase 2, a karamar hukumar Yola ta Kudu, ya kashe Nana Fadimatu, kwana guda kafin aurenta da sabon saurayin nata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hatsarin Jirgin Max Air: NSIB, NCAA Sun Shirya Gudanar Da Cikakken Bincike
A binciken da ‘yan sanda suka yi, ya nuna cewa wanda ake zargin ya dade suna tafka rikicin aure da marigayar.
An kuma samu labarin cewa su biyun sun amince su rabu da juna.
Sai dai kuma an ce Abubakar bisa ga tsananin kishin sa daya motsa kwatsam bayan ya samu labarin cewa matarsa da take kwana a gidansa zata auri wani Mahmud Rufa’i.
Bisa hakanne batare da bata wani lokaci ba yasa tabarya ya shekata.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya ce, “Abin da ya fusata da labarin cewa Nana za ta auri sabon miji ne, wanda ake zargin ya gayyaci tsohuwar matar tasa da misalin karfe 10 na dare wanda za’a daura mata aure a ranar 5 ga watan Mayu, 2023, inda ya shekata mata mari tare da dukanta da tabaraya sakamakon haka ta fadi a sume kuma daga baya aka ce ta mutu.”
Nguroje ya ce wanda ake zargin da aka kama, za a gurfanar da shi gaban kuliya bayan an tuhume shi.
A wani labarin kuma, PDP Ta Bukaci A Yada Zaman Shari’ar Kararrakin Zabe Kai Tsaye
Jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP da dan takararta a zaben shugaban kasa da aka kammala kwanan nan, Atiku Abubakar, sun shigar da bukatar neman odar bayar da damar yada labaran shari’ar kai-tsaye da suka kai zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, wanda za’a fara a yau.
A cikin bukatar da kungiyar lauyoyin sa karkashin jagorancin Chris Uche, SAN ta gabatar, ya bukaci musamman “Odar da ke ba da umarnin yin rajistar kotun da jam’iyyu kan yadda za a shigar da masu aikin yada labarai da kayan aikinsu cikin kotun.”