An tasa keyar Fatima Rahman mai shekaru 42 ‘yar asalin kasar Chadi zuwa gidan yari dake Ikoyi bisa zargin kashe kishiyarta Adizat a gidanta dake titin Alejo dake Ijede a yankin Ikorodu na jihar Legas,Tribune Online ta rahoto.
An gurfanar da Fatima da laifin kisan kai a wata kotun Majistare da ke Yaba a ranar Talata, 2 ga watan Mayu, 2023, a gaban mai shari’a P. E Nwaka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Ɗumi-Dumi: Gwamnan PDP Ya Kori Dukkan Kwamishinoni da Hadimansa
An ce ta fusata ne lokacin da ta gano cewa mijinta ya auri wata matar da ban bayan bayan ita.
Ana zargin ta je gidan matar mai ciki sanye da kayan aikin jinya kuma ta daba mata wuka inda ta hallakata har lahira.
Bayan da aka gano raunuka masu zurfi a wuyan marigayiyar da kai, an ce wani makwabcin marigayiyar da ya gan ta lokacin da ta isa gidan ya tuhume ta.
A cewar mai gabatar da kara, Thomas Nurudeen, wanda ake tuhuma, ta aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Afrilun 2023, da misalin karfe 12:40 na rana, a wuri ma lamba 43, layin Alejo dake kan titin Ijede, a Ikorodu, jihar Legas.
A cikin tuhume-tuhumen da ake yi, an ce ke Fatima Abdul Rahman, a ranar 9 ga watan Afrilu, 2023, da misalin karfe 12:40 na rana, a wuri mai lamba 43, layin Alero dake kan titin Ijede, Ikorodu, Jihar Legas a gundumar Majistare ta Legas, kin kashe wata Adizat Abdul Rahman, mai shekaru 28 ba bisa ka’ida ba, ta hanyar daba mata wuka kuma kin aikata laifin da ya saba wa tanadin sashe na 222 da kuma hukunci a karkashin sashe na 233 na dokar laifuka ta jihar Legas, Najeriya shekarar 2015.”
Sai dai kuma koyaya, ba a karɓi roƙon wanda ake tuhuma ba.
Mai gabatar da kara ya roki kotun da ta tasa keyar wanda ake kara zuwa gidan yari har zuwa lokacin da hukumar kula da kararrakin jama’a ta bayar da shawarar lauya.
Da yake bayar da wannan bukata, Nwaka ta tasa keyar ta zuwa Cibiyar Kula da gyaran hali ta Ikoyi tana jiran shawarar lauya.
Nwaka ya kuma dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 25 ga watan Mayu, 2023 domin yi mata shari’a.
A wani labarin kuma, Zaben Kananan Hukumomi: Gwamnatin Kwara Ta Kaddamar Da Hukumar Zabe
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya kaddamar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar a shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomin jihar.
Abdulrazaq ya bukaci mambobin hukumar da su gudanar da ayyukansu kamar yadda suka yi alkawarin rantsuwa da ofisoshinsu, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.