Wasu Sassan arewacin Indiya na fuskantar matsanancin guguwa mai ɗauke da sanyi wanda ya jefa yanayin rayuwar da al amurran yau da kullun cikin wani yanayi. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Rashin kyawon yanayin mai ɗauke da Hazo mai yawa ya jinkirta tashin jirage sama fiye da dari da kuma dakatar tafiyar dimbin jiragen kasa, lamarin da ya haifar da rudani a tashoshin jiragen sama da tashoshin jiragen kasar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ya Kamata Mata Su Rungumi Sana’ar Wanzanci – Na Bango
A ranar Lahadi Yanayin zafi ƙasar ta Indiya ya sauka zuwa maki 1.9 a mauaunin Celsius .
Wasu jihohin arewacin kasar na cigaba da fuskantar kalubalen matsanancin sanyin, inda yanayin ya sauka zuwa maki 6 a maauanin Celsius, ciki har da yankin Kashmir.
Mahukunta a babban birnin kasar Delhi sun umurci hukumomi da su ƙara hutun bazara tare da dakatar da koyarwa.
Ma’aikatar kula da yayani ta ƙasar ta ayyana samun matsanancin sanyi ne bayan da yanayin zafi ya sauka zuwa maki 4 a ma’auanin Celsius.
Ma’aikatar kula da yanayin ta umurci mutane da su dakatar ko rage aiwatar da wasu abubuwa har Izuwa lokacin da yanayin ya kyautata, haka kuma ta gargaɗi Mutane da suyi hankali sosai yayin da suke tuƙi a cikin wannan yanayi na hazo.
Haka kuma ana sa ran Yanayin ya haifar da wasu nau’o’ikan rashin lafiya mussamman a babban birnin ƙasar Delhi da ke fama da gurɓatance yanayi a ‘yan wattanin nan na hunturu.
Matsanancin sanyin ya shafi ‘yan ƙasar ta Indiya da basu da gidaje da ke kwana a gefen titinuna da tashoshin jiragen ƙasa.
A ranar Lahadin da ta gabata babban birnin ƙasar , Delhi ya yi fama ga daya daga cikin hazo mafi muni a tsawon kakar zuwa yanzu, tare da hazo mai yawa sosai wanda ya rufe sararin samaniyar birnin na tsawon sa’o’i masu yawa.
Rahotanni sun nuna cewa rashin kyan hangen nesa ya haifar da tsaikon tashin jirage sama da dari a filin jirgin saman Delhi yayin da aka karkatar da da dama daga cikin jiragen zuwa wasu wurare.
A ɓangaren sufurin Layin dogo na ƙasar ta Indiya – wanda ke ɗaukar fasinjoji kusan miliyan 23 a kullum – ya ce kusan jiragen ƙasa 29 ne ke sukayi zirga zirga a makare a arewacin Indiya.
An ci gaba da samun lalacewar yanayin a ranar Litinin inda aka ga motoci suna tafiya a hankali a kan tituna.
Kamfanin jiragen sama na ƙasar ta IndiGo ya wallafa a shafinsa na twitter cewa lamarin ya shafi lokutan tashi da saukar jiragen saboda hazo mai yawa da rashin gani da aka samu a Delhi, saboda haka ya shawarci fasinjoji da su duba tikitin tashin da saukar jirgin su kafin su isa zuwa filin jirgin.
Jami’ai sun ce suna sa ran Yanayin sanyi zai fara sauka daga ranar 10 ga watan Janairu nan.
A wani labari kuma, Gwamna AbdulRazaq Da Sarkin Ilorin Na Jimamin Mutuwar Shugaban Masu Rinjaye
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ya bayyana rasuwar shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Abubakar Olawoyin Magaji a matsayin abin bakin ciki da ban tsoro. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
A cikin sakon ta’aziyyar da babban sakataren yada labaran sa, Rafiu Ajakaye, ya fitar a Ilorin ranar Litinin, Gwamna Abdulrazaq ya kuma jajantawa iyalan tsohon shugaban masu rinjaye da kuma majalisar dokokin jihar Kwara ta 9, da kuma Sarkin Ilorin bisa rasuwarsa. .