Mambobin Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya zasu taro a Abuja a ranar Laraba domin tattaunawa akan wasu batutuwa masu amfani.
Shugaban Ƙungiyar kuma Gwamnan Jahar Ekiti Dr Kayode Fayemi wanda ya gayyaci Gwamnoni 36 domin taron, bai bayyana abunda aka shirya tattaunawa, wanda za’a fara daga ƙarfe 8 na dare, a Sakatariyar Ƙungiyar dake Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jagoran Jam’iyyar APC Na Kasa Kuma Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya
Shugaban Harkokin Al’umma na Sakatariyar Ƙungiyar Abdulrazaque Bello-Barkindo ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya sanyawa hannu.
A cewar takardar gayyatar da aka baiwa Darkta-Janar na Ƙungiyar Aishana Okauru, kuma a turawa Gwamnoni, wanda kuma shine na farko a shekarar 2022, zai kasance mutum da mutum, maimakon ta kafar sadarwa ta yanar gizo.
Wata majiya daga Sakatariyar ta Ƙungiyar tace Gwamnonin zasu tattauna akan matsalar tsaro dake fuskantar Jahohin dama ƙasa baki ɗaya.