Gwamnonin Arewa maso Gabas sun nuna damuwarsu kan wani sabon salo na karuwar ‘yan fashi da makami da ke kara tabarbarewa a harkokin tsaro a yankin.
Gwamnonin a karkashin kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun bayyana damuwar ne a wata sanarwar da suka fitar a karshen taron su karo na 8 da suka gudanar ranar Asabar a Maiduguri.
Sanarwar ta kara da cewa ayin da aka amince da nasarar da aka samu a kan ‘yan tada kayar baya, an kara wani sabon salo na ‘yan fashi da makami don ta’azzara matsalar tsaro a yankin.
KARANTA NANZamu Samar Da Shirin Yaki Da Jahilci A Najeriya-Ministan Ilimi
Sakamakon hadin gwiwar da sojoji ke yi na fatattakar ‘yan bindiga daga sassan kasar nan, a yanzu ‘yan bindigar sun koma yankin Arewa maso Gabas in ji kungiyar.
A cewar kungiyar, lamarin yana kara ta’azzara a Bauchi, Gombe da Taraba, wuraren da har ya zuwa yanzu babu ‘yan fashi da makami.
Daga nan sai kungiyar gwamnonin ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa baki cikin gaggawa domin shawo kan lamarin.
Kungiyar tana sane da cewa wasu sarakunan gargajiya da sauran hukumomin yankin suna hada kai da ‘yan bindigar, suna ba su mafaka da fakewa don aikata laifuka a yankin in ji su.
Gwamnonin dai sun yanke shawarar yanke hukunci a kan duk wani basaraken gargajiya ko shugaban al’umma da aka samu yana da alaka da ‘yan bindigar.
Kungiyar ta kuma kuduri aniyar gudanar da taron ta karo na 9 a Yola, jihar Adamawa tsakanin ranar Juma’a 3-4 ga Nuwamba, 2023.
A WANI LABARIN KUMA
Ba Zamu Lamunci Kisan Gilla Akan Jami’anmu Ba-IGP Egbotokun
Mukaddashin sufeto janar na yan sandan Najeriya Olukayode Egbotokun ya bayyana cewar hukumar yan sandan ba zata zuba ido tana kallon jami’anta suna mutuwa ta hanyar kusan gilla ba inda ya kara da cewar zasu dauki matakin da ya dace wajen ganin an kawo karshen wannan matsalar.