Tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce bai taba son zama dan siyasa ba, amma ya zama daya cikin hadari.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da kungiyar matasa karkashin kungiyar ‘Africa for Africa Youth Initiative’ (A4A), a dakin karatu na Olusegun Obasanjo (OOPL) da ke Abeokuta.
Ya ce ban taba son zama dan siyasa ba, na zama dan siyasa ne bisa bazata, amma son jama’a, son kasata da kuma bil’adama ya sa ya zama wani abu da na shigo ciki.
Ya bukaci yan siyasa da su yi burin shiga siyasa domin yi wa jama’arsu hidimaba wai don abinda zasu samu ba.
Karanta nanKungiyar Kwadago Ta Bukaci Gwamnati Ta Biya Musu Bukatunsu Daga Yanzu Zuwa Ranar Juma’a Ko Kuma
Da yake magana kan juyin mulkin da aka yi a wasu kasashen Afirka kwanan nan, Obasanjo ya bayyana cewa, ya kamata a kaucewa duk wani sharadi da ke karfafa juyin mulki a nahiyar yadda ya kamata.
Ya ce, ci gaba da juyin mulkin da sojoji ke yi a Afirka ya nuna cewa mutane sun gaji da wasu abubuwa a kasashensu, kuma suna bukatar mai ‘yantar da su.
Tsohon Shugaban kasar ya ce, ba zai goyi bayan juyin mulki ba duba da irin kwarewar da ya samu a hannun tsohon shugaban mulkin soja, marigayi Janar Sanni Abacha.
Ya yi kira ga gwamnatin kasashen Afirka daban-daban ciki har da Najeriya, da su tabbatar da cewa ba za su ingiza matasan ba har ta kai ga sun gwammace su kwace mulki da manufofinsu.
Ya ce da na sha wahala a hannun Abacha, ba zan goyi bayan juyin mulkin da sojoji suka yi ba. Amma idan ya zo, me za mu iya yi, kar ku manta musamman matasa, suna goyon bayan mafi yawan wadannan juyin mulkin.
Obasanjo ya yi kira ga shugabannin Afirka masu zaman dirshan da su canja ra’ayi, ya kara da cewa ya kamata a karfafa dimokuradiyyar da ke aiki ga kowa.
Kuma idan kun kasance a gwamnati tsawon shekaru 40 kuma ba ku gaji ba, watakila kuna buƙatar ritaya in ji shi.
A wani labarin kumaAlkalin Alkalan Najeriya Ya Bukaci Alkalai Da Suyi Taka Tsan Tsan Da Fasahar Zamani Wajen Yanke Hukunci
Obasanjo ya kuma yi kira ga matasan Afirka da su farka su rike mukaman shugabanci domin gobe da suke jira ba za ta taba zuwa ba.
A halin da ake ciki, daraktan shirin samar da matasa na nahiyar Afirka, Henry Akasisli, ya bayyana cewa ziyarar da suka kai wa tsohon shugaban kasar ta sake farfado da sha’awarsu da yunkurin daukar nahiyar Afirka zuwa mataki na gaba.