By Abbas Yakubu Yaura
Dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Kaduna a zaben daya gabata na shekarar 2019, Isa Ashiru, ya ce har yanzu yana da karfin sake tsayawa takara a babban zaben dake tafe na 2023 domin samar da ribar dimokuradiyya ga al’ummar mazabar sa.
Ya bayyana haka ne a lokacin wani taron karin kumallo da wasu abokan siyasar sa a Kaduna suka shirya a ranar Alhamis.
Ashiru, wanda ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben gwamna a shekarar 2019 amma aka tabka magudi, ya ce ba zai yi komai ba kuma ya bi tsarin da ya dace don samun nasara a zaben dake tafe na 2023.
Ya kuma jaddada cewa burinsa na yin mulki a jihar a jam’iyyar PDP ya tabbata.
“Ina da niyyar ci gaba har sai an samu nasara,” in ji shi.
Ashiru yayi wa’adi biyu a majalisar dokokin jihar sannan ya zarce zuwa majalisar wakilai, inda kuma ya sake yin wasu wa’adi biyu.
Sannan ya yi takara da gwamna Nasir El-Rufai a jam’iyyar APC a shekarar 2015 kuma ya sha kaye a zaben fidda gwani inda ya koma jam’iyyar PDP kafin gudanar da zaben shekarar 2019.
Ya zama dan takarar jam’iyayyar PDP, amma ya sha kaye a hannun El-Rufai.
Ashiru ya ce, “Abin sha’awa ne. A siyasa idan aka yi rashin nasara a karon farko ba asara ba ce.
“Wannan wasan ba game da ni bane, amma game da mutanena ne. Ina da hangen nesa, wanda na yi imani idan aka ba ni dama, zan canza rayuwar jama’ata zuwa mafi kyau.”