Tsohon kwamishinan lafiya na Nasarawa Abimiku ya rasu
Dr Bawa Ahmed Abimiku, tsohon kwamishinan lafiya a jihar Nasarawa ya rasu.
Wata majiya mai tushe wacce ta tabbatar da hakan, ta bayyana cewa Abimiku, wanda kuma ke rike da sarautar Durbin Eggon, ya yi fama da doguwar jinya da sanyin safiyar ranar Talata, 19 ga watan Disamba, a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Keffi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kirsimeti: Jami’an Civil Defense 1,200 Aka Tura Jahar Adamawa
Ya taka muhimmiyar rawa a fannin kiwon lafiya, inda ya yi aiki a matsayin kwamishina kuma memba a majalisar zartarwa ta jiha a zamanin gwamnatin marigayi Alhaji (Dr) Aliyu Akwe Doma.
Za a yi jana’izar Abimiku a babban masallacin Abuja, FCT, da karfe 2:00 na rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
A wani labarin kuma:Kirsimeti: Jami’an Civil Defense 1,200 Aka Tura Jahar Adamawa
Wani jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya ce shugaba Bola Tinubu ba zai zama shugaban kasa da na jihohi ba.
Momodu ya ce shiga tsakani da Tinubu ya yi a rikicin da ke tsakanin Gwamna Sim Fubara na Jihar Ribas da Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT, Nyesom Wike bai dace ba a doka.