Tsohon Ministan ayyuka na musamman, Alhaji Bello Kirfi, ya maka gwamnatin jihar Bauchi a kotu domin kalubalantar tsige shi daga mukaminsa na babban dan majalissar sarki a masarautar Bauchi.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Kirfi, ma’aikacin gwamnatin tarayya mai ritaya, kuma minista a gwamnatin Alhaji Shehu Shagari a shekarun 1980 sannan kuma ministan ayyuka na musamman a lokacin gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo a shekarun 2000, an cire masa sarautar gargajiya ta Wazirin Bauchi.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamnatin Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Barkewar Cutar Ebola A Fadin Kasar
“kuma Majalisar Masarautar Bauchi ta cire shi daga zama dan majalissar sarki karo na biyu a cikin shekaru biyar bisa zargin “rashin biyayya da mutuntawa” ga Gwamnan Jihar, Bala Mohammed.
An isar da tsige Basaraken ne a wata takarda da Sakataren Masarautar Bauchi Alh. Shehu Mudi Muhammad,ya fitar mai kwanan wata 3 ga watan Janairu, 2023 mai lamba: BEC/ADM/20/VOL.XV mai taken: “Cirewa daga ofis a matsayin memba na dan majalissar sarki da sarautar gargajiya na Wazirin Bauchi.”
Muhammad ya bayyana a cikin wasikar tasa cewa ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu ta sanar da majalisar masarauta ta Kirfi “rashin biyayya da rashin mutuntawa” ga gwamna, wanda hakan ya sa aka cire shi daga mukaminsa.
Ya ce: “An umurce ni da in koma ga wata wasika da aka samu daga ma’aikatar harkokin kananan hukumomi mai lamba: MLG/LG/S/72/T mai kwanan wata 30 ga watan Disamba, 2022. Abin da ke cikin wasikar ya nuna rashin aminci da rashin mutunta ku. zuwa ga Gwamnan Jihar da gwamnati. Don haka ya ba da umarnin cire ku tare da sakamako nan take.
“Saboda abubuwan da suka gabata, an cire ka daga mukamin Wazirin Bauchi da kuma dan majalissar sarkin masarautar Bauchi.”
Sai dai a wata sanarwa mai dauke da sa hannun dansa kuma mai magana da yawunsa, Yakubu Kirfi, kuma aka rabawa manema labarai a ranar Laraba, tsohon ministan ya ce ya garzaya kotu ne domin kalubalantar tsige shi.
“Batun cirewa a matsayin Wazirin Bauchi kuma dan majalisa a ranar 3 ga watan Janairu 2023 da gwamnatin jihar ta shirya ta hanyar masarautu, babu shakka ya haifar da cece-kuce a cikin jihar da kewaye. Don haka jama’a daga sassa daban-daban suka yi tururuwa zuwa gidan Alhaji Muhammad Bello Kirfi domin ziyarar jaje da nuna goyon baya.
“Ba tare da wata shakka ba, a halin yanzu maganar tana gaban kotun da ta dace, wadda za ta tantance sahihancin matakin da gwamnatin jihar ta dauka. Kawo yanzu dai babu wata sanarwa da aka fitar a hukumance daga Alh. Muhammad Bello Kirfi CON,” ya rubuta.
Ya kuma karyata labarin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa cewa mahaifinsa ya sha alwashin tsige gwamna Bala Mohammed a zaben 2023 saboda ya kawo shi ofis.
Ya ce labarin ba shi da tushe kuma ba na gaskiya ba ne, yana mai nuni da cewa a matsayinsa na musulmi, ya yi imani da cewa Allah ne ke ba da mulki, kuma ya karbi abinsa lokacin da ya ke so.
Yakubu, tsohon kwamishinan shari’a kuma babban lauya a gwamnatocin Mohammed Abubakar da Bala Mohammed, ya ce, “An ja hankalinmu ga buga jaridu a ranakun 8 da 9 ga watan Janairu, 2023, da wasu Kungiyoyin Kafafan Yada Labarai suka yi ta ambato Alh. Dr. Muhammad Bello Kirfi CON ya ce zai tsige Gwamna Bala Abdulkadir Muhammed (Kauran Bauchi) a zaben gwamnan jihar Bauchi da ke tafe.
“Labarin bashi da tushe kuma ba na gaskiya bane. A addinance kuma, a matsayinmu na masu qarfi a cikin labarin Imani, mun yi imani da mulki na Allah ne shi kadai, yana bayar da shi ga wanda ya so, kuma ya karba a lokacin da ya ga dama”.
A wani labarin kuma, Jami’a a Najeriya Ta Haramtawa Dalibai da Ma’aikata Sanya Tufafi Masu Nuna Tsiraici
Jami’ar Godfrey Okoye da ke jihar Enugu ta haramta sanya suturar da ba ta dace ba tare da bullo da sabbin ka’idojin tufafi ga dalibai da ma’aikata domin tantancewa cikin sauki.
Mataimakin shugaban jami’ar, Rev. Fr.Christian Anieke, ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin da yake jawabi ga ma’aikatan da daliban makarantar yayin da suke dawowa daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara.