Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari Ya Amshi Baƙuncin Tsaffin Jami’an sa
Wasu manyan tsaffin Jami:an Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun kai mai ziyara a Daura.
KARANTA WANNAN LABARIN:Rikicin Ribas: Na Hannun Daman Wike, Chidi Amadi ya yi murabus a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fubara
Tsaffin Jami’an Gwamnatin ta Buhari da su ka kai mai ziyara gaisuwa da nuna har yanzu ana tare sun hada da tsohon shugaban ma’aikatan fadarshi Farfesa Ibrahim Gambari, tsohon mai bashi shawara ta fuskar tsaro Babagana Mongono da kuma sai kuma tsohon shugaban hukumar fasa kwari ta Custom Hamid Ali.
Duk da dai basu wata ganawa ta musaman da yan jarida ba, amma sun bayyana cewa ziyara ce su ka kawo ga maigidan na su dan gaishe shi da yi ma shi fatan alkhairi