Madam Obebhatein Jonathan kanwar tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Ebele Jonathan ta rasu.
Ta rasu ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu, 2024, a cibiyar lafiya ta tarayya dake Yenagoa, jihar Bayelsa, bayan gajeruwar rashin lafiya, tana da shekaru saba’in.
KARANTA WANNAN LABARIN: NANS ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta sa baki kan shirin kara kudin makaranta
Wata sanarwa da ofishin yada labarai na Jonathan ya fitar ta nuna cewa marigayiyar wadda aka fi sani da Amissi malama ce mai ritaya, ’yar kasuwa, uwa mai kauna kuma kakarta wacce ta yi sadaukarwa ta hidima ga Allah da kuma bil’adama.
Ita Kirista ce mai ibada, mace tagari kuma abin koyi ga mutane da yawa a ciki da wajen al’ummarta.
Sanarwar ta kuma nuna cewa an shirya binne gawar ranar Talata 16 ga watan Fabrairu, 2024, inda ta jaddada cewa iyalan za su sanar da cikakkun bayanai game da jana’izar.
Madam Obebhatein Jonathan ta rasu ta bar ‘ya’ya uku, ‘yan’uwa, ciki har da Dokta Goodluck Ebele Jonathan, da mahaifiyarta Mama Eunice Afeni-Jonathan.
A wani labarin kuma:Gwamnatin Najeriya za ta inganta tsaro domin farfado da dazuka – Minista
Gwamnatin tarayya ta ce za ta inganta tsarin tsaron kasar domin kwato dazuzzukan kasar.
Ministan Muhalli, Balarebe Lawal ne ya bayyana hakan a wani taron koli da aka gudanar a Kaduna, ranar Alhamis.