Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC ciki har da ‘yan kwamitin zartarwa na jam’iyyar a karamar hukumar Obingwa da ke gundumar Abia ta kudu a jihar Abia sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP mai mulki.
Tsohon shugaban jam’iyyar APC na shiyyar, Orji Chikezirim da tsohuwar shugabar mata ta APC, Mrs Adaku Abel sune suka jagoranci wadanda suka sauya shekar zuwa jam’iyyar PDP reshen Abia tare da shugabannin kananan hukumomin APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: An Sako Dan Tsohon Shugaban Kasar Iran Bayan Shafe Shekaru Bakwai A Gidan Yari
Wadanda suka sauya sheka sun shiga jam’iyyar ne a lokacin yakin neman zaben Gwamna Okezie Ikpeazu na takarar Sanata a karshen mako.
Tsohon shugaban jam’iyyar na shiyyar Abia ta kudu, Orji Chikezirim ya ce nasarar Ikpeazu ya kai su ga sauya sheka.
Da yake karbar wadanda suka sauya sheka a madadin reshen Abia na jam’iyyar PDP, Ibe Nwadioha ya baiwa sabbin ‘ya’yan jam’iyyar tabbacin samun daidaito da walwala.
A wani labarin kuma, Mun Shirya Gudanar Da Zaben Zagaye Na Biyu — Shugaban INEC
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Mahmood Yakubu ya ce mai yiyuwa ne a je zagaye na biyu a zaben shugaban kasa bayan da masu kada kuri’a suka kada kuri’unsu a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 ga ‘yan takarar da suke so. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Shugaban zaben ya ce INEC ta shirya tsaf domin gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa idan har ba wanda ya yi nasara bayan zaben neman zuwa Aso Rock na watan gobe.