Allah ya yi wa Professor Ibrahim Halilu Umar, rasuwa a wannan rana ta Litinin.
DIMOKURAƊIYYA ta rawaito cewa Marigayin tsohon Shugaban Jami’ar Bayero Kano ne kuma Shugaban Majalisar Yada Ilmin Addinin Musulunci ta Jihar Kano.
KU KARANTA: Yadda Aka Cashewa Tinubu A Taron Tattaunawa Na NBA
Ya dai zama shugaban jami’ar BUK ne daga 1979 zuwa 1986, kuma ya rike mukamai na matakin ilimin boko, daban daban domin kuwa ya kai matsayin ganganran a bangaren boko.
Za dai ayi masa jana’iza ne a gobe Talata da karfe goma na safe a Kofar Kudu, wato kofar fadar Sarkin Kano.
Wata Sanarwa daga Ahmed Aminu
Kakakin Hadakar Ma su Kishin Kano ya ce Marigayin ya kuma rike mukamai daban daban na kungiyoyin ci gaban kasa a Kano da sauran jihohin Najeriya.
A wani labarin kuma: EU Ta Turo Jami’ai Na Musamman Domin Sanya Ido Kan Zaben 2023
Tawagar kungiyar Tarayyar Turai masu sanya ido kan zaben kasar nan, ta ce za a tura masu sa ido 100 a zaben shekarar 2023.
Babban jami’in sa ido, EU EOM, Barry Andrews ne ya bayyana haka a yayin kaddamar da kungiyar EU EOM ga Najeriya 2023, a Abuja ranar Litinin.