Wata bazawara mai shekaru 75, Mrs. Dorothy Onwudirimba, ta zargi dan uwanta mai suna Okonkwo da korar ta da karfi daga gidan mijinta tare da lalata kadarorin gidan a ranar 6 ga watan Disamba.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, kakar ta yi zargin cewa Okonkwo ya samu umarnin kotu ne ba tare da saninta ba na lalata muhimman kadarorin gidan a garin Umuntumogu da ke karamar hukumar Okwuohia Obowo a jihar Abia.
KARANTA WANNAN LABARIN: FG Tayi Kuskure Wajen Zargin Gwamnoni Da Kawo Talauci – Tsohon Shugaban Hukumar NHIS
A wani faifan bidiyo, an ga bazawarar tana kuka yayin da wasu mazaje suka cire rufin gidan suka watsar da kadarorinta a waje.
Da take ba da labarin abin da ya faru da ita, uwar ‘ya’ya biyar ta ce;
“A ranar Talatar da ta gabata, ina gida sai kafintoci da jami’an ‘yan sanda dauke da bindigogi suka shiga harabar gidanmu suka fara cire rufin gidana. Na yi mamaki na fara tambayarsu me yasa suke cire min rufin gida, amma ba su ba ni amsa ba.
Sa’ad da ’yan sanda suka bar gidanmu, ɗaya daga cikin ’ya’yana mai suna Chinonso, ya shiga gidan ya fara zubar da dukiyata. Ni da ’ya’yana mun yi asarar kayayyakinmu da yawa, har da kuɗi.
Bayan haka, dan autana ya kulle mu a wajen gidan, kuma a yanzu mun makale a unguwarmu; surukata da ta haihu kwanakin baya tana wani wuri da jaririnta alhalin ina gidan wani.”
Kakar ta ce ta sanar da basaraken al’ummar yankin lamarin, inda ta bukaci gwamnati ta kawo mata dauki.
A wani labarin kuma, 2023: Zan Umurci CBN Ya Dakatar Da Yawan Canjin Kudi Idan Aka Zabe Ni – Atiku
Gabanin zaben shugaban kasa da ke tafe, dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce zai umurci babban bankin Najeriya, CBN ya dakatar da tsarin musayar kudaden kasashen waje.
Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a shirin gidan talabijin na Channels na “The People’s Townhall” wanda DAILY POST ke sawa ido.
Samun kudaden waje ya kasance babban kalubale ga masana’antu da masu kasuwanci a Najeriya.