Wata mata ta labarta yadda aurensu ya kare da wani fasto wanda labarin ya taba zuciyar kowa, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
A cewarta, ta fara haihuwa ne da wuri, inda ta haifi yara biyu wanda daga bisani mijinta, wani fasto, ya bukaci su rabu bayan Ubangiji ya umarce shi da yin hakan.
Yayin da wasu ke ganin kamar raina mata hankali yayi, wasu kuma sun bata hakuri inda su ka ce kansa yayi mawa, su na mata fatan alheri.
Matar mai amfani da subs @fockosi, mai shekaru ashirin da daya, 21 ta yi aure da wuri inda yanzu haka take da yara har biyu da karancin shekarunta.
Ta bayyana yadda ta auri wani fasto yayin da take tsakanin shekaru 15, wanda lokacin da ta cika shekaru 16 ta haifi danta na farko.
Ta ce ta haifi na biyun lokacin tana da shekaru 17. Ta ci gaba da bayyana yadda watarana ya falka yace ya ji cewa Ubangijinsa ya yi masa wahayi, inda ya umarce shi da ya sake ta, ya auri mata.
A cewarta bayan nan ne ya amshe yaran guda biyu ya sake ta. Ganin wannan lamarin ne ya sanya ta yanke shawarar komawa makaranta.
Ta ce ta kammala Diploma yanzu haka, kuma tana sa ran nan ba da jimawa ba ta kammala digirinta.
Kungiyar CAN ta yi Allah-wadai da kisan Faston ta, ta bukaci Gudanar da bincike
Shugabancin Ƙungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta kasa ta yi Allah-wadai da yunkurin kashe Janar Overseer na Omega Fire Ministries International, Apostle Johnson Suleman, tare da kashe mataimakansa da jami’an tsaro.
Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wata sanarwa.
“Muna daukar hakan a matsayin wani abu mai tada hankali da kuma wani yunkuri na miyagun ayyuka na haddasa fitina a jihar Edo kadai, har ma da kasa baki daya.
“Shugabannin Ƙungiyar CAN na kasa suna jajantawa kungiyar Omega Fire Ministries International da kuma iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan mummunan lamari.
“Yayin da muke kira da a gudanar da cikakken bincike kan wannan mugunyar aika-aikar da ta lakume rayukan mutane da dama, bari kowa ya tashi tsaye domin bankado sunayen wadanda ke da hannu a wannan danyen aikin tare da gurfanar da su a gaban kotu,” inji Okoh.
Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro da su dauki lamarin a matsayin wata alama ta tsarin tsaro na kasa baki daya, kuma a gaggauta magance lamarin.
Ya ce, “Hakazalika, bisa la’akari da gargadin ofishin jakadancin Amurka na yiyuwar harin ta’addanci daga ‘yan bindiga a Abuja, kungiyar ta CAN ta yi kira ga jami’an tsaron mu da su farga da kalubalen tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a domin gujewa illar da za a iya samu a wajen neman kai. -taimako.
“Dole ne mu yi duk abin da ya kamata don hana masu shirya makircin kawar da ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba a duk inda suke a cikin kasar nan ta hanyar muguwar dabi’a, daga cimma burinsu na jahilci. Kada a bar su su ci gaba da muguntarsu.”
Yayin da ya bukaci majami’u da kuma sauran ‘yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan tare da fadakar da jami’an tsaro duk wani yunkuri da ake da su a yankunansu, Okoh ya ce kungiyar za ta ci gaba da yin addu’o’in samun zaman lafiya da tsaro a kasar nan.