Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi maraba da sako ‘yan mata hudu da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jihar Borno.
‘Yan matan da aka sako da sauran wadanda akai garkuwa da su, an sace su ne daga yankin Kautikari a farkon watan nan a karamar hukumar Chibok.
A cikin wata sanarwa da Asusun ya fitar a ranar Litinin, UNICEF ya bayyana jin dadi shi kan ‘yancin ‘da yan matan suka Sami a ranar Lahadi.
Wakilin UNICEF a Najeriya, Peter Hawkins, ya ce “UNICEF ta yi matukar farin ciki ga ‘yan matan da aka sako Kuma aka sada su da iyalansu.”
Ya ci gaba da cewa, “labari ne mai dadi cewa ‘yan matan sun dawo tare da sada su da iyalansu da abokansu.”
“Amma abin bakin ciki, yara da dama a arewa maso gabashin Najeriya sun ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa; musamman wadanda rikicin Boko haram ya shafa.
“Yara suna da ‘yancin samun muhalli mai aminci, lafiya, ilimi da ‘yanci daga cin zarafi da azabtarwa – duk abin da ke cikin matsala lokacin da suke cikin bauta.”
A cewar UNICEF, kimanin Yara 173 daga cikin ‘yan matan Chibok ne har yanzu ba a gansu ba. A watan Janairu, an kuma sace da yawa a Pemi, wata al’umma a karamar hukumar Chibok.
Da yake Allah wadai da sace mutanen da kuma yin kira da a sake su, Hawkins ya ce, “Yara ba ganimar rikici ba ce. Duk yaran da aka yi garkuwa da su dole ne a gaggauta sakin su ga iyalansu.”