Basaraken Masarautar Owo ta Olowo, Oba Ajibade Ogunoye, ya bayyana takaicin sa dangane da harin da wasu bata gari suka kai kan wata Coci Lahadi da ta gabata.
Oba Ogunoye yayin wata hira ta musamman da Punch tayi da shi a karshen makon ya bayyana cewa, duk wani mai son ganin bayan mabiya kowane addini tabbas wannan mutum ba zai yi nasara ba.
A cewar sa, kai hari kan masu ibada a lokacin da suke tsaka da Ibada abu da maras imani ne kadai zai iya aikatawa, dan haka yace duk wanda ya san da hannunsa a harin da akai kaiwa cocin to ya jira yaga yadda karshen sa zata kasance.
Da aka tambaye shi kan irin kokarin da sukai lokacin faruwar abun ya bayar da amsa da cewa:
Mun yi kira da babbar murya ga daukacin jami’an tsaro, da nufin ganin sun dauki matakin lalubo masu hannu a wannan aika aika, kuma ba laifi suna kokari kan abinda ya dace.
Daga nan sai ya jaddada kiran sa ga gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu kan ya ci gaba da nuna kulawa ga al’ummar sa, duba da cewa lokacin da abun ya faru baya gari yana Abuja, amma cikin hanzari ya koma domin jajantawa wanda abun ya rutsa da su.
A karshe ya bukaci gwamnatin kan ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen kare masu ibada a wuraren ibadar su, domin kowa ya samu kwanciyar hankali yayin ibada.