Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, wadanda suka yi garkuwa da wani limamin coci mai ritaya, Rev Filibus Bamai na cocin ECWA, Matuak Rimi, a masarautar Moro’a a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna, sun bukaci a biya su Naira miliyan daya domin a sake shi.
Wata majiya dake kusa da cocin ta ba da wannan bayanin a Manchok ranar Talata.
Karanta nanFilato: Kakakin Majalisa Abbas Ya Yi Allah-Wadai da Sabbin Kashe-Kashen Da Aka Yi
Majiyar ta ce Bamai wanda ya yi ritaya daga aiki a ranar 17 ga watan Disamba bayan ya cika shekaru 65 na ritaya, an sace shi ne a ranar Lahadi da karfe 12:50 na safe a gidansa.
Majiyar ta ce, an tafi da malamin ne da gajeren wando kawai a jikinsa, yayin da aka yi wa matar sa dukan tsiya da sanda aka yi mata raunuka da kuma tambo a bayanta.
Majiyar ta ce masu garkuwa da mutanen sun fara neman Naira miliyan 5 domin a sako shi, inda ya ce tun a ranar Litinin din da ta gabata sun rage kudin fansa zuwa Naira miliyan daya.
Malamin ya ce kawo yanzu an tattara kimanin Naira 300,000, ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kara tsaurara matakan tsaro a yankin domin kare rayuka da dukiyoyi.
A wani labarin kumaDole Ne Mu Hada Kai Don Tabbatar Da Zaman Lafiya a Najeriya — Tinubu Ga gwamnoni
Adadin sace-sacen mutane na karuwa a yankunan karkara inda masu garkuwa da mutane ke cin gajiyar rashin tsaro wajen daukar wadanda abin ya shafa yadda suka ga dama.
An yi garkuwa da wani manomi a kauyen Pari da ke cikin masarautar Chawai a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna, Mista Sunday Bage, mako guda da ya gabata tare da matarsa, Listu.