Kungiyar Malaman jami’o’i a Nigeria ta shawarci gwamnatin tarayya da cewa ta cika alkawuransu da ta dauki nauyin ganin ta gabatar, ko kuma su dauki matakin garkame jami’o’in baki daya tare da ci gaba da gudanar da yajin aikin da suke yi yanzu haka.
Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya bayyana haka a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu a ranar Lahadi, ya dage cewa dole ne gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar a shekarar 2009.
Osodeke ya bayyana haka ne yayin mayar da martani ga Ministan Kwadago, da amar da Aiki da Samar da Albarkatun Kasa, Dakta Chris Ngige, wanda a wata hira da gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da kudaden da za ta iya cika nauyin da ya rataya a wuyanta a yarjejeniyar da ta kulla da ASUU.
Ngige ya ce gwamnati na duba yiwuwar sake tattaunawa kan sharuddan yarjejeniya da ASUU a kokarin kawo karshen yajin aikin da malaman jami’o’in ke yi.
Sai dai shugaban kungiyar ASUU na kasa, Osodeke, ya ce duk wani abu da ya shafi inganta da saka hannun jari a jami’o’in, gwamnati za ta ce ba ta da kudi.
“Yaran talakawa za su sha wahala a jami’o’in Najeriya yayin da ‘ya’yansu za su samu ilimi mai kyau a wajen kasar. Lokacin da suka wuce, sai su dawo nan su ɗauki ayyuka masu daɗi a nan, kuma su ci gaba da sarauta akan ɗiyan talakawa. Batun aji ne. A gare mu, zabin su ne; sun rufe jami’o’i gaba daya, su bar duk yaran su je su koyi makanikai ko kuma su ba da kudin jami’o’in.”
Ya kuma mayar da martani kan kalaman Ngige na cewa gwamnati na kira da a sake tattaunawa kan yarjejeniyar 2009 da ta rattabawa ASUU.
Osodeke ya ce, “Ba mu sanya hannu kan wata yarjejeniya da su ba. Su aiwatar da abin da suka amince da shi shekaru 13 da suka gabata. A wancan lokacin ana samun canjin dala daya zuwa kasa da N100.00, amma yanzu farashin ya kai dala daya zuwa sama da N500.00. Hatta darajar waccan kudin kafin mu amince a 2019 tuni ta zube.
“Mun gama tattaunawa, amma idan sun koma wurin shugabanninsu cewa akwai wani yanki da ya kamata mu duba, za mu duba, a shirye