Ma’aikatar Hajji da Umrah a Saudiyya ta fitar da jeren ƙa’idoji da matakan ba da damar gudanar da Umrah da salloli a watan Ramadan a masallatan Makkah da Madina.
Daga ciki allurar rigakafin korona ya wajabta, domin ba za a amincewa duk wani musulmi da bai yi wannan allurar ba ya shiga masallacin Makkah da Madina.
Sannan za ake amfani da wata manhaja ta musamman da aka samar domin tantace mutanen da suka karɓi rigakafin da wadanda ba ayi wa ba, da kuma sanin matakin lafiyar mutum.
Sannan ba za a amince yaran su shiga ko doshi harabar masallatan ba a bana.
Akwai kuma tarar Riyal dubu 10, kan duk wani mutum da ya karya ƙa’idar gudanar da Umrah ba tare da samu amincewa ba, da kuma tarar dubu 1 kan duk mutum da ya yi ƙoƙarin shiga masallaci ba tare da izini ba.
Sannan ba za a ke wuce minti 30 ba wajen gudanar da sallah Taraweeh da Tahajudd a dukkanin masallatan da ke faɗin ƙasar.
Wannan matakai na zuwa ne bayan Sarki Salman ya fitar da sanarwar cewa ya bayar da umurnin rage raka’o’in sallar Taraweeh a Masallacin Harami na Makkah da kuma na Madina.
Ma’aikatar dai ta tunasar da mutane amfanin bin matakai kariya daga kamuwa daga cutuka.