By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 6 ne suka mutu a ranar litinin bayan wani bam da aka dana a gefen hanya ya lalata wata karamar motar bas yayin wani harin kwantan bauna da wasu mahara suka kai a arewa maso gabashin Kenya kusa da kan iyaka da kasar Somaliya, in ji ‘yan sanda.
Maharan sun bude wuta kan motar mai dauke da kujeru 14 bayan da ta bi ta kan bam din mai tazarar kilomita takwas daga garin Mandera.
Kakakin ‘yan sandan kasar Bruno Shioso ya ce “Mutane shida ne suka mutu a yayin harin da aka kai kan wata mota.””Ana ci gaba da gudanar da aikin tsaro domin zakulo maharan.”
Kawo yanzu dai babu wani wanda yayi da’awar alhakin kai harin.
Wani rahoton ‘yan sandan ya ce, tawagar ‘yan sintiri ta Janar din ‘yan sandan da ke kan kafa da kuma kusa da su, sun yi artabu da maharan, wadanda suka tsere zuwa kan iyakar Somalia.
Majiyar ta kara da cewa, maharan sun yi amfani da bindigogi da kuma gurneti a yayin kai harin.
Karamar motar bas wacce gabaki daya ta kama a harin na dauke da fasinjojin da ba a san adadinsu ba.
Shioso ya shaida wa AFP cewa mutane bakwai sun tsira amma sun sami “raunuka iri-iri”.
Yankin Mandera na da saurin kai hare-hare a kan iyakar kasarsa mai tsayi tsakanin ta da Somaliya, inda kungiyar masu kishin Islama ta Al-Shabaab ke iko da yankunan karkara.
Sauran yankunan da ke makwabtaka da Somaliya su ma na fuskantar hare-hare kuma jami’an Kenya kan yi gaggawar dora alhakin kai hare-hare a kasarta.
Kasar Kenya ta sha fama da munanan hare-haren kungiyar Al-Shabaab a matsayin ramuwar gayya kan tura sojojinta zuwa Somaliya a shekara ta 2011 a matsayin wani bangare na rundunar Tarayyar Afirka domin fatattakar mayakan jihadi.
Kenya ita ce babbar mai bayar da gudunmawar sojoji a cikin tawagar Tarayyar Afirka a Somaliya.
A shekara ta 2015, wani hari da aka kai a wata jami’a a Garissa, wani yanki mai iyaka da Somaliya, ya yi sanadin mutuwar mutane 148, kusan dukkansu daliban makarantar ne lamarin ya rutsa dasu.
Ofisoshin jakadancin Faransa da Jamus sun yi gargadin kai hari cikin kwanaki, yayin da Amurka ta fitar da wani sabon gargadi na tsaro.AFP