Rahotanni sun bayyana cewa dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya tsallake rijiya da baya a wani harin da ‘yan bindiga suka kai a hanyar Warri-Sapele. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Lamarin, a cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Dennis Otu, ya fitar ya faru ne a ranar Lahadi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Karancin Kudi: Ka Dakatar da Emefiele a matsayin Gwamnan CBN – Mataimakin Tinubu ya shawarci Buhari
Otu ya ce Oborevwori ya je Osubi ne daga Sapele lokacin da lamarin ya faru, ya kara da cewa an kai rahoto ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A wani bangare na harin da ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba suka kai wa ayarin dan takarar gwamnan PDP na jihar Delta, Rt Hon Sheriff Oborevwori, a ranar Lahadi, 12 ga Maris, 2023, sun fuskanci mummunan hari.
Sanarwar ta kara da cewa Oborevwori ya tsallake rijiya da baya da yardar Allah, inda ya bayyana cewa yana tafiya ne a cikin wata mota mai sulke.
A wani labarin kuma, Jam’iyar ADC Ta Kori Dan takaranta na Gwamna a wata Jiha, Ta ce a zabi PDP
Jam’iyar African Democratic Congress, ADC, ta kori dan takararta na gwamna a jihar Jigawa, Muhammad Sani Gumel, bisa zargin yiwa jam’iyar zagon kasa.
Shugaban riko na jam’iyyar a jihar Jigawa Kabiru Hussaini ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Dutse babban birnin jihar.