Jami’in ‘yan sandan (DPO) na sashen ‘yan sanda na Seme a jihar Legas, SP Mojeed Salami, ya yanke jiki fadi ya mutu a ofishinsa a ranar Talata. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ko da yake ba a san ainihin musabbabin mutuwar ba, wata majiya ta ‘yan sanda da ta zanta da wakilin majiyar mu a jiya ta ce a baya DPO din ya yi korafin cewa yana fama da ciwon kai kuma ya tafi asibiti.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Gwamnan Arewa Ya Amince Da Karin Hutun Kwanaki 8 Ga Makarantu
Ya ce bayan ‘yan sa’o’i ne DPO ya koma ofishinsa ya ci gaba da aiki, amma bayan sa’o’i sai ya kira shi ya yi korafi.
Majiyar ta ce, “Ya bukaci umarninsa da ya kira jami’in kula da laifuka (DCO). Ina tsammanin yana so ya mika wa DCO ragamar gudanarwar ofishin ne
Kakakin ‘yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce, “Ya rasu ne a ranar Talata.
” Abin ya ba kowa mamaki domin babu wani abu mai tsanani game da lafiyarsa.”
“Sun ce kawai ya koka da wani karamin ciwon kai, ya je asibiti, ya dawo, ya fara aiki kuma ya mutu ba da jimawa ba.” inji shi