- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya umurci ma’aikatar lafiya da ta yi bincike tare da kamo wasu ma’aikatan lafiya.
- Daukar matakin kan ma’aikatan lafiyar ya biyo bayan zargin kin karbar wadanda hatsari ya rutsa da su.
- Gwamnan yace Idan duk wani likita ko wani ma’aikaci ba ya son zuwa wurin marasa lafiya to ya kamata a kore shi ba tare da wani jinkiri ba.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya umurci ma’aikatar lafiya da ta yi bincike tare da kamo ma’aikatan lafiyar da ke bakin aiki bisa zargin kin amincewa da wadanda hatsarin ya rutsa da su asibitin Umaru Shehu Ultra Modern Hospital da ke Maiduguri,Tribune Online ta rawaito.
Zulum ya bayar da umarnin ne a ranar Alhamis a sashin bada agajin gaggawa na asibitin.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Kano Ta Ce Ba Zata Ja Da Baya Ba Kan Yin Rusau
A cewarsa, “abin da ya faru bai dace ba kuma ba za a yarda da shi ba.”
Ya kara da cewa ya ziyarci asibitin ne domin mayar da martani ga wani faifan bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta wanda ke nuna yadda wasu jami’an kiwon lafiya suka ki amincewa da wadanda hatsarin ya rutsa da su da aka kawo asibitin a rana da lokaci da masu bincike za su tantance.
Ya ba da sa’o’i 24 ga ƙungiyar bincike don gano ma’aikatan kiwon lafiya da abin ya shafa da kuma ba da shawarar takunkumin da suka dace.
“Yanayin da aka bar marasa lafiya suna kuka don neman taimako, amma asibiti ya ƙi basu kulawar data dace? Ba za mu ƙyale irin wannan yanayin ya maimaita kansa ba.
“Ban ga dalilin da zai sa ba za a dauki matakin ladabtarwa a kan ma’aikatan da suka yi kuskure a wannan asibitin ba,” in ji gwamnan.
“Idan duk wani likita ko wani ma’aikaci a kowane ɗayan wurarenmu ba ya son zuwa wurin marasa lafiya ba tare da wani dalili ba, to ya kamata a kore shi ba tare da wani jinkiri ba,” in ji Zulum.
Ya kara da cewa, “A cikin sa’o’i 24 masu zuwa, ya kamata hukumar kula da asibitoci da ma’aikatar lafiya ta binciki lamarin tare da tabbatar da daukar matakan ladabtarwa ga duk wadanda ke bakin aiki da suka ki karbar wadanda hadarin ya rutsa da su.”
Gwamna Zulum ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zuba jari sosai a fannin kiwon lafiya, ciki har da jin dadin jami’an kiwon lafiya a fadin jihar, don haka ya yi kira ga jami’an kiwon lafiya da su mayar da hankali wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga duk majinyata ba tare da nuna bambanci ba.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Kano Ta Kwashe Tan 400 Na Sharar Gida Cikin Sa’o’i 72
Gwamnatin Kano ta yi nasarar kwashe fiye da tireloli 400 na sharar gida a cikin kwanaki uku da fara gudanar da aikin.
Daukar matakin shine don tabbatar da yadda ake zubar da shara a manyan titunan da kuma hana toshe magudanan ruwa.
Hakan zai kawar afkuwar ambaliyar ruwa, musamman a yanzu da muke cikin lokacin damina.