Gwamnatin jihar Borno ta fara daukar malamai 3,000 aiki a makarantun gwamnati dake fadin jihar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Wata sanarwa da mukaddashin sakataren a ma’aikatar ilimi, Ali Musa, ya fitar, ta karfafa wa duk masu sha’awar neman aikin da kuma suka cancanta su nema ta hanyar kafar yanar gizo mai suna: www.moeapplication.bornostate.gov.ng
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Ortom, Wike Sun Kaucewa Haduwa Da Atiku A Makurdi
“Mu na sanar da jama’a cewa ma’aikatar ilimi ta jihar Borno ta fara daukar malamai 3,000 aiki.
“Duk masu sha’awar neman ilimi da ke son bunkasa fannin koyarwa za su iya neman aikin koyarwa a makarantun gwamnati dake fadin jihar Borno.
“Wajibi ne wadanda za su nemi aikin sukasance sun kammala karatunsu a manyan makarantun kuma ba su wuce shekaru 50 ba, su mallaki takardar shaidar yi wa kasa hidima wato (NYSC ko makamancinsa), kuma sukasance a shirye suke a tura su kowane bangare na jihar,” in ji Musa.
Ya kuma ce gogewa, ta hanyar samun mallakar takaddar shedar kwarewa a fannin koyarwa da ilimin na’ura mai kwakwalwa za yi alfanu wajan neman aikin.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa za a rufe shafin ne da aka bude a ranar 5 ga Disamba, a ranar 31 ga Disamba shwkarar 2022.
A wani labarin kuma, Za Mu Fara Koyar Wa Daliban Firamari Fasahar Hada Shafin Yanar Gizo Da Manhaja— Shugaban Kenya
Shugaban kasar Kenya William Ruto ya bayyana cewa, nan ba da jimawa ba za a fara koyar da Daliban kasar fasahar mu’amullar hada Shafin yanar gizo da Manhaja wato Coding a turance, a makarantun Firamari zuwa Jami’a. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a taron baje kolin fasaha da kirkire kirkire na kasar wanda Wakilan Kamfanin Meta, Microsoft da Google suka halarta.
Ya kara da cewa, Wannan shirin na da manufar bunkasa matasan kasar ta fukar fasahar zamani
Sai dai wannan na zuwa yayin da yunkurin Kenya na samarwa Yan makarantan Furamari Kannan Kwamfuta ya citura tun a shekarar 2013.
Kana kasar na fama da karanci Kayayyakin aiki a makarantun Firamari, Rashin Kwararrun Malamai da kuma zarge zargin cin hanci da rashawa a bangaren ilimi