By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa wani hatsarin mota ya afku a filin shakatawa na Asaba, Upper Iweka ta hanyar Awka zuwa Onitsha a ranar Lahadi.
Motoci 5 ne suka yi hatsarin wanda ake danganta shi da gazawar birki.
A cewar wani shaidan gani da ido, wani direban motar DAF mai lamba XC 416 PK, ya rasa yadda zai yi, sakamakon shanyewar birki da ya yi, wanda hakan tasa ya murkushe wasu motoci a baya.
Kimanin mutane 22 ne da suka hada da manya maza 13, manya mata bakwai, yaro namiji daya da mace daya hatsarin ya rutsa dasu.
Mutane biyu ne suka mutu a hatsarin yayin da mutane 11 suka samu raunuka.
Har izuwa lokacin da ake hada wannan rahoto, tawagar masu aikin ceto na gwamnatin tarayya sun garzaya da wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Toronto, Boromie.
Likitan dake bakin aiki ya tabbatar da mutuwar wadannan manya maza biyu.
An ajiye gawarwakin mamatan a dakin ajiyar gawa na asibiti.
Kwamandan hukumar FRSC na jihar, Adeoye Irelewuyi, ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu.
Ya bukaci masu ababen hawa su tabbatar da cewa motocinsu sun bi ka’idojin tsaro kadan kafin tuki.
Sannan Ya kara da cewa “Dole ne a bi ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa a kowane lokaci.”