Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kebbi, Ahmed Magaji-Kontagora, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan rasuwar ASP Shu’aibu Sani-Malunfashi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Nafi’u Abubakar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Birnin Kebbi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Dawo Daga Kasar Koriya Ta Kudu
Ya ce, a ranar 19 ga watan Oktoba, ASPAbdullahi Garba, jami’i mai kula da ofishin ‘yan sanda na Sauwa, ya samu sabani da mamacin, jami’in da ke kula da laifuka na reshen Argungu.
Kakakin ya bayyana cewa, a yayin fafatawar da suka yi a gaban shagon Garba, ya caka wa Sani-Malunfashi wuka a haƙarƙarinsa na hagu da almakashi.
Jami’in ‘yan sandan shiyya, Argungu, ya garzaya wurin da lamarin ya faru, inda ya damke jami’in da ya aikata laifin, sannan ya kwato baje kolin (makaman dake hannun sa).
DPO din ya garzaya da Sani Malunfashi zuwa asibitin Sir Yahaya Memorial da ke Birnin Kebbi, inda wani likita ya tabbatar da rasuwarsa.
A yanzu haka Abdullahi Garba na tsare a hukumar binciken manyan laifuka ta jihar (CID) dake Birnin Kebbi. An kuma mika karar zuwa sashin kisan kai.
CP Magaji-Kontagora ya aika da tawagar manyan jami’an ‘yan sanda domin ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokanan dan sandan da ya rasu. Ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya ba shi aljanna.
A wani labarin kuma, Zabar Jam’iyyar APC Shine Zabar Zaman Lafiya – Dan Takarar Gwamna
Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Filato, Nentawe Yilwatda, ya jaddada aniyarsa ta inganta rayuwar mata da matasa da kuma nakasassu a jihar idan har aka zabe shi a zaben 2023.
Yilwatda ya yi alkawarin zai zama gwamnan kowane dan kasa ba tare da la’akari da kabila ko addini ba.