Wani jigon jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya roki gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi da ya fice daga jam’iyyar (APC).
Sowunmi, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2019, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin (Politics Today) ranar Juma’a a gidan Talabijin na Channels.
“Idan har zan dauki kowa daga APC… Ina ganin zan kalli Yahaya Bello,” in ji shi yayin da yake amsa tambaya kan wanda zai goyi bayan ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, idan ba dan babbar jam’iyyar adawa ba ne.
“Me yasa? Shi (Bello) matashi ne, ya shiga akwatin ku. Ya kasance gwamna. Ina kallon irin abubuwan da yake yi, na karanta irin mutanen da suke goyon bayansa, amma na san yana cikin jam’iyyar da ba za su taba kallonsa ba.
“Don haka kila kawai in ce wa abokina Yahaya, ‘Zo PDP; ko da ba ka samu Shugaban kasa ba, wata rana za mu maishe ka shugaban kasa a jam’iyyarmu’. Amma idan kun kasance tare da wannan jam’iyyar, ban amince da su ba. Ba sa son matasa… kawai abin da suke sha’awar shi ne kuntata musu akan abin da suke fassara a matsayin Najeriya a yanzu. ”
A daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke hasashen tsarin zaben wani shugaba da zai zama mafi kololuwa a kasar, ‘yan siyasa da jam’iyyu sun fara zage-zage wajen ganin an zabo dan takararsu ya gaji shugaban kasa.