Wani shugaban rundunar hadin gwiwa ta Civilian Task Force (CJTF) a jihar Borno ya mutu sakamakon fashewar wani abu da ake kyautata zaton nakiyoyin da mayakan Boko Haram suka binne..
Wasu mutane biyar sun samu raunuka a lamarin da ya faru a karamar hukumar Biu ta jihar Borno.
Har zuwa rasuwarsa, Ibrahim Maliya Saidu, marigayin, shi ne sakataren tsare-tsare na rundunar Sakai ta CJTF a Biu.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a kusa da kauyen Maliya, unguwar Mandaragarau a garin Biu.
A cewar babban jami’in CJTF Mohammed Aliyu, marigayi Maliya jajirtacce ne da ya yi yaki da ‘yan tawayen a lokuta da dama.
“Mun sami labari mai ban tausayi da yammacin yau, cewa daya daga cikin mafi kwazo a membobinmu na CJTF ya mutu yayin da ake gudanar da aiki. abin takaici ne ga kowa. Allah ya jikan wadanda suka rugamu gidan gaskiya.”
“Ka huta lafiya, dan uwana Ibrahim Maliya Saidu Maliya, tare da wasu abokanmu, ciki har da Docta Suleiman Sykami, wanda shi ma ya taka wasu bama-bamai da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka binne.”