Wani Likita ya Yanke jiki ya faɗi har ya rasa Ran shi, bayan shafe awonni 72 yana aikin Tiyata
Likitan da ke aiki a Asibitin Koyarwa ya ta jihar Legas Umoh Michael ya rasu ne bayan ya share awonni saba’in da biyu 72 yana tiyata a sashen gudanar da Tiyata na Asibitin.
Likitocin masu neman ƙwarewa a ranar Talata lokacin da suka aikewa Babban likitan asibitin sun bayyana rashin jindadin su akan mutuwar abokin aikin nasu.
Haka kuma sunyi zargin cewa abokin nasu ya rasu ne a sabili da ƙarancin abinci da makwanci mai kyau da ya rasa a lokacin gudanar da aikin shi a asibitin.
Sun kuma nuna matuƙar damuwa akan yadda ɗan’uwan nasu ya rasa ranshi bayan aikin da yayi ba tare da hutawa ba.
Dr Michael dai ya shafe awonni 72 ne yana aiki, inda ya bar ofishin da misalin karfe 3 na dare domin yin shirin zuwa Cocin, inda daga isar shi Cocin ne ya yanke jiki ya fadi, daga bisani kuma rai yayi halin shi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Munada Dabarun Yaki Da Zasu Iya Kawar Da Matsalar Tasaro A Najeriya-Hafsan Sojoji
Abokan kwanan Dr. Umoh Michael sun ce, zai wuya kaga shi a ɗaki yana bacci, domin mafi yawan lokuta yana a bakin aiki ne.
“Wurin zaman likitocin tilas ne ya zama kyauta ga Ma’aikata, Masu rijista da marasa rijista, yakamata su sa aikin ya zama mafi aminci a gare mu Bai ɗaya, bai kamata ace komai mu za muyi ba, ” likitocin suka rubuta.
A wani labarin kuma:Tinubu Ya Bukaci Yan Najeriya Mazauna Amurka Da Su Dawo Gida Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya karfafa gwiwar yan Najeriya a Amurka da su tashi tsaye daga gazawa ta hanyar sauya tunaninsu don samun nasara a dukkan al’amuransu na rayuwa.
Tinubu ya ba da wannan shawarar ne a wajen taron gidan shugaban kasa da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje a ranar Laraba a birnin New York.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NiDCOM) ce ta shirya taron a