Wani manomi mai suna Adnan Sani, a ranar Alhamis, 22 ga watan Disamba, ya kai karar wata kawar matarsa Saudat Bagobiri gaban kotun shari’a da ke zamanta a Kaduna bisa zarginta da sace masa wasu awakai guda hudu.
Wanda ya shigar da karar ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ta taba mayar masa da guda biyu daga cikin akuyoyinsa da suka bace, ta kuma bukaci ya bata aron namijin Talotalo domin ta samarwa tamatar Talotalonta miji.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Dalilin da Yasa Osinbajo Ya Ziyarci Dan Takarar Shugaban Kasa Tinubu
“Waɗannan awaki biyu da ta dawo da su sun sake bacewa, sai muka tarar da wata akuya tawa a daure a gidanta.
Mai karar ya kara da cewa “Ta mayar da namijin Talotalon amma ina zarginta da sace awakina guda hudu, sai ta yaudari matata ta dauka cewa kawarta ce, kawai ta kusance matata don ta sace mana dabbobin mu.” Inji shi.
A nata bangaren, wadda ake kara ta ce ba ta san komai ba game da bacewar awakin.
“Na iske akuya daya tana yawo a harabar gidana saboda nima ina kiwon akuya, da na samu akuyar sai na kira shi nace ya duba ko akuyar tasa ce, sai ya tabbatar da cewa lallai tasa ce, sai ya dauki akuyar ya tafi,” inji ta. .
Sai dai da yake yanke hukuncin Alkalin kotun, Salisu Abubakar-Tureta, ya yi watsi da karar yana mai cewa duk ikirarin da mai karar ya yi zato ne kawai.
Alkalin ya sallami wanda ake tuhuma.
A wani labarin kuma, 2023: Peter Obi Ya Mika Wuya Ga Gazawa Tare Da Gwamnonin Da Suka Gaza – Jigon Jam’iyyar APC
Shugaban jam’iyyar APC mai suna Ogenyi Okpoku, ya yi ikirarin cewa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) ya mika wuya ga gazawarsa, yana mai cewa mambobin yakin neman zabensa sun gaza.
Ogenyi ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a shirin Siyasar Gidan Talabijin na Channels a Yau Alhamis da yamma.
Ya yi zargin cewa Obi na da alaka da wasu gwamnonin da suka gaza a jihohinsu daban-daban.