By Abbas Yakubu Yaura
An gano wani matashi dan shekara 25 mai suna Olakunle Obaoye a rataye a wani daji a kauyen Erinmope da ke kusa da Ayedun a karamar hukumar Oke Ero a jihar Kwara.
Marigayin dai kamar yadda majiyar ‘yan uwa ta bayyana, ana zargin ya kashe kansa ne saboda rashin iya biyan basukan da da mutane suke bin sa.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, reshen jihar Kwara, Babawale Afolabi, ya ce an tsinci gawar marigayin a wani daji a ranar Litinin.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ranar Litinin, 17 ga watan Janairu, 2022, da misalin karfe 12:00 na rana, wani Thomas Obaoye, mazaunin garin Ayedun, ya je ofishin sashin mu da ke yankin domin sanar da mutanenmu game da rasuwar dan uwansa, Olakunle Obaoye, mai shekaru 25, wanda ya rasa ransa. an tsinci gawar a rataye akan bishiyar a wani abu kamar na kashe kansa.
“Bayan rahoton, jami’an NSCDC na sashen Ayedun sun je wurin da lamarin ya faru, inda suka yi aiki tare da ‘yan uwan mamacin wajen sauke gawarsa daga kan bishiyar.
“Daga baya an mika gawar ga dangin don yi musu jana’iza yadda ya kamata.”
Babawale ya ce an mika lamarin ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma daukar matakan da suka dace.