Wani dan kasuwa, Mista Justine Onu, a ranar Alhamis, ya bukaci wata kotun gargajiya da ke Jikwoyi, Abuja, da ta raba aurensa da matarsa, Joyce, bisa zarginta dayin almubazzaranci.
Mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa matarsa ba ta san yadda ake tafiyar da al’amuran gida yadda ya kamata ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Babban Kwamandan ‘Yan Awaren Kasar Kamaru A Jihar Taraba
“Matata ba ta san cewa abubuwa suna da wahala a ƙasar ba. A duk lokacin da ta yanke shawarar yin abinci, sai ta yi girki da yawa kuma abincin ana zubar dashi ne cikin shara,” inji shi.
Mai shigar da karar ya kuma shaida wa kotun cewa matarsa ta kasance mai yawan karuwanci kuma ya gaji da auren.
Onu ya sanar da kotun cewa ya kamu da cutar hawan jini ne saboda zargin yin lalata da matarsa take yayi yawa.
Ya kuma yi zargin cewa matarsa ba ta da alhaki kuma ba ta kula da yaran.
Sai dai wadda ake kara, Joyce, ta musanta dukkan zarge-zargen, kuma alkalin kotun, Labaran Gusau, ya dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 17 ga watan Nuwamba.NAN
A wani labarin kuma, Zargin Almundahanar Kudade: Gwamnan Zamfara Ya Baiwa Hukumar EFCC Damar Bincikar Kadarorin Jihar
Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, ya yi tayin baiwa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC damar shiga tare da binciken kadarori a cikin jihar, wanda ta yi zargin cewa an same shi da makudan kudade domin yin almundahana, ta hanyar biyan albashi a hannu.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara ya fitar, ya ce matakin ya zama dole ne biyo bayan abin da ya bayyana a matsayin babban hadin kai da makiyan jihar Zamfara suka yi na bata sunan gwamnan da kuma ci gaban da gwamnan ya samu wanda tuni ya umurci lauyoyinsa da su sanar da shi a hukumance. matsayin hukumar, ciki har da kiraye-kirayen a janye labaran karya da kafar yanar gizo ta SaharaReporters ta yi a kan nasa.