Wasu da ake zargin makiyaya ne sun kai hari Okeluse a karamar hukumar Ose ta jihar Ondo a daren Lahadi.
Makiyayan, an tattara su ne suka kai wa al’ummar garin hari da misalin karfe 10 na daren Lahadi
Rahotanni sun ce makiyayan sun kashe manajan wani gidan mai da ke garin
An wallafa bidiyon gawar sa a Facebook a cikin jini a malale.
Idan dai za a iya tunawa an kashe mutane uku a garin Omolege da ke wannan yanki makonnin da suka gabata.
Matsalar tsaro ta kara ta’azzara a jihar a ‘yan kwanakin nan inda gwamnati ta maido da kudirin ta na kamo wadanda suka aikata laifin.