Wasu fusatattun matasa sun kona makarantar da masu garkuwa da mutane suka sace Hanifa Abubakar suka binne gawar ta a Kano.
Makarantar mai zaman kanta, mai suna Noble Kids Comprehensive College, tana Kwanar Dakata a karamar hukumar Nassarawa, cikin birnin Kano.
An sace Hanifa Abubakar ne a ranar 2 ga watan Disamba ta hannun malaminta, Abdulmalik Tanko, wanda kuma shi ne mamallakin makarantar mai zaman kanta.
An kama Abdulmalik Tanko tare da rufe makarantar da gwamnatin jihar ta yi.
Kakakin ‘yan sanda a Kano, Abdullahi Kiyawa, ya ce fusatattun matasan sun kona makarantar a cikin dare.
Ya ce ba a samu asarar rai ba a lamarin, amma an kona sassan ginin makarantar.
Mista Kiyawa ya kara da cewa har yanzu rundunar ‘yan sandan ba ta kama wani da ake zargi da faruwar lamarin ba.