By Abbas Yakubu Yaura
An samu barkewar tashin hankali a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Osun da ke Osogbo a ranar Laraba, yayin da wasu fusatattun‘yan daba suka mamaye harabar domin neman gawar abokin su da aka jiye a dakin ajiyar gawa na asibitin a ranar Talata.
An tattaro cewa fusatattun ‘yan dabar da suka isa a kan babura, a ranar Talata sun jefar da gawar daya daga cikin su da aka kashe a Osogbo a asibiti.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa Yace Ba Zai Barwa Ahmad Lawan Tikitin Kujerar Sanata Ba
Sun bukaci a sako musu gawar ba tare da wani takarda ba.
Rikicin ya yi kamari ne lokacin da ma’aikatan asibitin suka ce da ‘yan dabar za su cika wasu takardu kafin abasu gawar wanda ya sa ‘yan barandan suka fusata a lokacin.
‘Yan ta’addan, wadanda suka fito fili suna nuna rashin amincewar da matakin, sun kuma yi barazanar haifar da hargitsi matukar ba a sako musu gawar ba.
Da yawa daga cikin ma’aikatan asibitin da ‘yan uwa da majinyata da ke dakunan kwanan majinyata da sauran wadanda ke da sana’o’i a harabar a lokacin da ake gudanar da wasan kwaikwayo, ana iya ganinsu suna ja da baya daga wajen da ‘yan iskan suka taru don gudun kada a far musu a rikicin da ya biyo baya.
Daga baya wasu jami’an ‘yan sanda dauke da makamai sun isa asibitin inda suka fatattaki ‘yan bindigar daga harabar.
Da aka tuntubi shugaban kwamitin ba da shawara kan likitoci na asibitin, Dakta Babatunde Afolabi, ya ce an shawo kan lamarin.
Afolabi ya bayyana cewa an gudanar da bincike a kan gawar kuma an dauko gawar domin binne ta.
Comments 1