Wani matashi mai suna Marwan Abubakar da kuma wani Iliyasu Abubakar an tsare su a gidan yari dake garin Yola na jihar Adamawa bisa zargin su da kutsa kai gidajen mutane da satar kayayyaki masu daraja.
Daily Post ta rahoto cewa babbar Kotun Majistare da ke zama a Yola ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare mutanen biyu bayan sun amsa laifukan da ake tuhumar su da su.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: INEC Ta Gabatar Da Shaida Ta Farko Kan Karar Atiku da PDP
Yayin da yake gurfanar da wadanda ake tuhumar tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Insifekta S.S. Nicholas, ya shaida wa kotun cewa;
Masu laifin Marwan da Iliyasu Abubakar mai shekaru 19 sun aikata laifukan da ake tuhumarsu ne a ranar 12 ga watan Yunin 2023.
Ya kara da cewa lokacin da wadanda ake kara su biyun da wani Ibrahim Mallam babban wanda ake zargi sun kutsa kai gidan wata mata Aitiya Wesley da ke Kofare tare da kwashe wasu kayayyaki da dama.
Ya yi zargin cewa ‘yan ukun sun kutsa kai cikin gidanta inda suka yi awon gaba da wayar hannu, agogon hannu guda takwas, wasu sili na rufi, da tufafin da suka kai tsabar kudi Naira N611,000.
Mai gabatar da kara ya kuma yi zargin cewa Marwan da Musa Muhammed a ranar 10 ga watan Yunin 2023 sun kai farmaki gidan wani Emeka Oneyi da Ugochukwu na Demsawo inda suka kwace wayar da ta kai zunzurutun kudi Naira N65,000 da kuma tsabar kudi N7,500.
Ya ce a yayin gudanar da bincike, wadanda ake tuhumar sun ambaci Ibrahim Mallam da Sabiu Musa wadanda a halin yanzu suke hannun su a matsayin wadanda ake zargin.
Insfekta Nicholas ya shaidawa kotun cewa har yanzu ba a kammala binciken ba saboda sauran wadanda ake tuhuma suna hannunsu.
Alkalin kotun, Alheri Ishaku ya tasa keyar Marwan da Iliyasu bisa laifin hada baki, fashi da makami, fasa gidaje da kuma sata.
Daga baya alkalin kotun ya dage sauraron kararrakin biyu zuwa ranar 10 ga watan Yuli, 2023, don ci gaba da saurare.
A wani labarin kuma, Kotu Ta Umarci PSC Da Ta Biya AIG Mai Ritaya Diyyar Miliyoyi
Kotun kolin da’ar ma’aikata ta kasa a ranar Litinin ta umurci hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda da ta biya mataimakin babban sufeto janar na ‘yan sanda Joseph Mbu mai ritaya zunzurutun kudi naira miliyan 40 a matsayin diyya.
Biyan kamar yadda mai shari’a Osatohanmwen Obaseki-Osaghae ya ba da umarnin, na yin murabus ne bisa tilas ga Mbu ba bisa ka’ida ba kafin ya cika shekaru 60.