By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan fashi sun kashe mutane hudu a kauyen Amangwu da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.
Mutanen hudu da aka kashe sun hada da wata tsohuwar shugabar mata ta jam’iyya PDP, Ucha Ndukwe, da diyarta, Chibuzor Ndukwe, da wasu mutane biyun, Ndubuisi Ndukwe da Kalu Umah.
‘Yan sanda a jihar sun tabbatar da cewa an harbe su ne a ranar Talata.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Ohafia, Dokta Okorafor Ukiwe, ya ce ya je Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya dake Umuahia, inda ya je ya ga wata da aka kwantar da ita a asibiti,da diyar matar da ta rasu, Madam Ndukwe. Ya kara da cewa, “Matar da ta samu rauni ta rasa mahaifiyarta da ‘yar uwarta wadanda ‘yan bindigar suka harbe tare da ita a gidansu.
“An dai yi mata tiyata domin cire harsasan da ke jikinta.
‘Yan bindigar sun kashe uwar yarinyar wanda itace shugabar mata ta jam’iyyar PDP da kuma ‘yar uwarta a gidansu bayan sun kona shagon mahaifiyarta.”
Ya ci gaba da cewa wadanda ake zargin sun fusata ne da cewa matar mai sayar da abinci ta sabawa ayyukan da suke yi a cikin al’umma, ya kara da cewa, “Sun kona shagon, suka zo gidanta suka harbe ta, yayin da ‘ya’yanta mata biyu suka fito sai ‘yan fashin suka harbe su.
“Daya ta mutu nan take yayin da dayar da ta samu raunin harbin harsashi aka garzaya da ita asibiti kuma tana samun kulawa a sashin kula da lafiya.Sannan ‘yan bindigar sun kashe wasu yara maza biyu,” in ji shugaban karamar hukumar.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Geoffrey Ogbonna, ya ce, “Mun ji haka amma muna jiran rahoton da zai taimaka wa ‘yan sanda sanin cikakken bayani kan lamarin.”