Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kashe Udeng Ibrahim Yamusa, basaraken masarautar Yukuben da ke karamar hukumar Takum a jihar Taraba.
Gidan Talabijin na Channels ya tattaro cewa ‘yan bindigar sun kuma kashe direban sa wanda shi ma dan sa ne.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kafin kashe wadannan mutane, ‘yan bindigar sun yi garkuwa da basaraken gargajiya da dansa ne a ranar Alhamis a wani kwanton bauna a lokacin da suke komawa gida daga Takum, shedikwatar karamar hukumar Takum.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, dansa na farko wanda kuma shi ne sakatarensa Fasto John Ibrahim, ya bayyana cewa an yi wa wadanda aka kashen kisan gilla a kan hanyarsu ta komawa masarautar.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/kotu-ta-%c9%97aure-wani-mutum-kan-canja-%c6%99wayar-paracetamol-a-matsayin-chloroquine-a-kano/
“Waɗannan da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kama mahaifina da ɗan’uwana ba tare da saninsu ba. Sun yanke shawarar tafiya ne a kan babur suna barin motarsa ta hukuma saboda lalacewar hanyar da ta yi,” inji shi.
Basaraken, wanda ya ce zai halarci taron zaman lafiya a Takum, ya yanke shawarar komawa gida ne saboda an dage taron.
Ibrahim ya kasa sanin dalilin da ya sa ‘yan bindigar da suka addabi al’ummomin yankin Raya Musamman na Yangtu, Takum da Ussa, suka yanke shawarar katse rayuwar mahaifinsa da dan uwansa a lokaci guda.
A yayin da ya bukaci jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa don gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika, ya kuma bukaci a tura sojoji yankin kudancin jihar Taraba.
Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Kwache Gambo ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a daren ranar Asabar din nan.
Ta ce an gano gawar basaraken da dansa ne a wani daji a wata unguwa mai nisa da inda aka yi garkuwa da su.
A cewar Gambo, an fara gudanar da bincike kan lamarin kamar yadda kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarta domin bankado wadanda suka aikata kisan.
Kakakin ‘yan sandan ta kuma bukaci mazauna yankin da su rika kai rahoton duk wani motsi ko barazana ga rayuwa da wuri don baiwa ‘yan sanda damar shawo kan lamarin.