Daga: Muhammad Gambo Damaturu
A yayin da wa’adin karbar tsofaffin takardun kudin Naira ke kara karatowa wasu ‘yan kasuwa a Gashua sun garkame shagunan su don gudun karbar tsofaffin kudin.
Hakan ya fito daga bakin wasu mazauna garin wadanda suka tattauna da wakilin Jaridar Dimokuradiyya a Gashua, Shelkwatar Karamar hukumar Bade.
KARANTA WANNAN LABARIN: Duk da Kakkausan Gargadin CBN: Har Yanzu Bankuna Na Sanya Tsofaffin Takardun Naira a ATM
Gashua na daya daga cikin manyan biranen jihar Yobe da suka yi fice a fannin kasuwanci.
Saura kasa da kwanaki goma wa’adin daina karbar tsoffin kudaden da aka sauyawa launi wanda suka kunshi Naira 200, 500 da 1000, wasu ‘yan Kasuwa a Gashua, Shelkwatar Karamar hukumar Bade dake jihar Yobe suka soma rufe shagunan su da wuraren sana’o’in su don gujewa karbar tsoffin kudaden.
Tuni wannan lamari ya jawo hauhawa farashin kayan masarufi.
Saidai wata majiya mai karfi ta shaidawa Jaridar Dimokuradiyya cewa ba’a dauki wani tsawon lokaci ba, Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Suleiman ya yi gargadi ga masu shagunan da cewa kada su ki karban kudaden har sai Lokacin da Babban Bankin Najeriya ta kaiyade ya iso.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa karancin Bankuna a yankin shine babban matsalar da tasa mutane suke cikin zullumi.
A wani labarin kuma, CBN Ya Bai wa Bankuna Isassun Sabbin Takardun Kudin Naira – Jami’i
Shugaban Babban Bankin Najeriya CBN reshen jihar Ogun, Alhaji Wahab Oseni, ya bayyana cewa babban bankin ya samar da isassun takardun kudade ga bankunan kasuwanci a fadin kasar nan domin cika wa’adin da aka tanada na tsoffin takardun kudaden.
Oseni ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a wurin taron wayar da kan jama’a kan sabbin kudaden da ake samu a kasuwar Awolowo, Sagamu.